Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedJami’an tsaro sun yi ajalin ‘yan ta’addan Lakurawa a jihar Kebbi

Jami’an tsaro sun yi ajalin ‘yan ta’addan Lakurawa a jihar Kebbi

Nasir Idris 

Rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a jihar Kebbi ta yi nasarar halaka wasu da ake zargin ‘yan Lakurawa ne, yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka, a wani sumame da suka kai a kauyukan Rubin Bisa da Fana da ke karamar hukumar Dandi a jihar Kebbi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan tsaro, Abdulrahman Zagga, ya fitar a Birnin Kebbi babban birnin jihar.

Abdulrahman Zagga ya ce an gudanar da aikin ne a ranar Larabar da ta gabata, bisa rahotanni da bayanan sirri da aka samu.

Biyo bayan korafin da shugaban karamar hukumar Dandi, Dakta Mansur Kamba, ya gabatar mako daya da ya gabata, dangane da ayyukan ‘yan bindigar a kauyukan Fana da Rubin Bisa,kuma an kwato manyan makamai daga hannun wadanda ake zargin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata