Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuJam‘iyyar APC ta lashe kujeru 20 cikin 23 a zaben kananan hukumomin...

Jam‘iyyar APC ta lashe kujeru 20 cikin 23 a zaben kananan hukumomin jihar Rivers

Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da aka gudanar a ranar Asabar.

Ita kuwa jam’iyyar da ke mulki a jihar wato PDP, ta samu nasara a kananan hukumomi uku kacal a zaɓen da hukumar zaɓen mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta gudanar.

Gwamna Siminalayi Fubara ma ya sha kaye a mazabarsa ta karamar hukumar Opobo-Nkoro inda babbar jam’iyyar adawa ta jihar ta yi nasara.

Shugaban RSIEC, Dr. Michael Odey, ne ya bayyana sakamakon a ofishin hukumar da ke kan titin Aba Road a birnin Fatakwal, a ranar Lahadi da rana.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata