DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedJam'iyyar APC za ta karbi Kano a zaben 2027 – Akpabio

Jam’iyyar APC za ta karbi Kano a zaben 2027 – Akpabio

 

Godswill Akpabio

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce jam’iyyar APC za ta karbi mulki a jihar Kano a shekarar 2027.

Akpabio ya bayanna haka ne a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya kai ziyara ga mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado.

Ya ce da muhimman ayyukan da Sanata Basheer Lado ke yi a jihar, Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje,  APC na kara samun nasara a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa a halin yanzu jihar na karkashin jam’iyyar NNPP, inda Abba Kabir Yusuf ke a matsayin gwamna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata