Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedJam'iyyar NNPP a Nijeriya ta bukaci El-Rufai ya nemi afuwarta bisa zargin...

Jam’iyyar NNPP a Nijeriya ta bukaci El-Rufai ya nemi afuwarta bisa zargin da ya yi mata

Tsohon gwamnan jihar Kaduna 

Jam’iyyar NNPP ta kasa ta yi Allah-wadai bisa zargin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi wa jam’iyyar cewa gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyinta dangane da korar tsohon dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso da kuma dakatar da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Sakataren jam’iyyar na kasa, Oginni Olaposi, ne ya yi wannan Allah-Wadai ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Ta cikin sanarwar NNPP ta zargi El-Rufai, da kokarin kawar da hankalin mutane daga ainihin abubuwan da ke faruwa yanzu haka.

Tsohon gwamnan na Kaduna wanda a baya-bayan nan ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa SDP, ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya ce ke rura wutar rikicin jam’iyya mai mulki da kuma na jam’iyyun adawar kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata