DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeBabban LabarinmuJam'iyyar NNPP ta ce ba ta tare da Kwankwaso a shirinsa na...

Jam’iyyar NNPP ta ce ba ta tare da Kwankwaso a shirinsa na komawa APC

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa shirin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar na komawa jam’iyyar APC bisa sharadi ba ya da alaka da ita, illa dai wani yunkurin ne nasa da ya shafi kungiyar siyasar Kwankwasiya.

A wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa Dr. Ogini Olaposi ya fitar a ranar Litinin a Legas,ya ce jawabin Kwankwaso na ranar Asabar cewa shi da magoya bayansa sun shirya shiga APC, bisa sharadin ba za su yarda a yi amfani da su wajen lashe zabe a watsar da su daga baya ba.

A cewar sanarwar tuni jam’iyyar ta kori Kwankwaso da magoya bayansa daga NNPP saboda cin amanar jam’iyyar, yanzu ba shi da jam’iyya domin yawancin magoya bayansa a Kano sun riga sun koma APC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata