Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuJam'iyyar PDP ce kawai za ta iya ja da Tinubu a 2027...

Jam’iyyar PDP ce kawai za ta iya ja da Tinubu a 2027 – Sakon Wike ga sabuwar hadakar ADC

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi masu adawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yin amfani da wahalar da ’yan Najeriya ke fuskanta a matsayin makami na siyasa, yana mai cewa jam’iyyar adawa ta PDP ce kaɗai ke da ikon kalubalantar Tinubu a 2027, muddin ta magance rikicin da take ciki.

Wike ya bayyana hakan ne yayin taron sa da ’yan jarida na wata-wata da yake gudanarwa a Abuja a ranar Alhamis.

Ya caccaki shugabannin da suka taba riƙe madafun iko a baya, yana cewa yawancinsu sun yi shiru ko kuma sun kasa saukaka rayuwar talakawa lokacin da suke kan mulki.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata