Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuJiga-jigan ADC sun jagoranci zanga-zangar “ceto dimokuraɗiyya” a Abuja

Jiga-jigan ADC sun jagoranci zanga-zangar “ceto dimokuraɗiyya” a Abuja

Manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC sun jagoranci zanga-zangar “ceto dimokuraɗiyyar Najeriya” a birnin Abuja.

Daga cikin waɗanda suka halarci zanga-zangar akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola.

Haka kuma, tsohon gwamnan Anambra Peter Obi ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su fito domin kare dimokuraɗiyya.

Rahotannin da gidan talabijin na Channels ya tattaro sun ce zanga-zangar ta fara ne daga yankin Maitama, inda masu zanga-zangar suka nufi hedikwatar Hukumar zaben Nijeriya INEC.

Jagororin ADCin dai na zargin INEC da nuna son kai ga jam’iyyar APC mai mulki, abin da suka ce na barazana ga dimokuraɗiyyar ƙasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ɗauki alluna masu ɗauke da saƙonni da ke cewa “ku nisanci kotunanmu” da kuma kira da a bai wa dimokuraɗiyya damar numfashi.

A yayin zanga-zangar, Rotimi Amaechi ya riƙa jawabi daga cikin mota yana ƙarfafa masu zanga-zangar su ci gaba da tafiya cikin lumana.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya ce zanga-zangar na nufin nuna adawa da abin da ya kira nuna bangaranci daga hukumar zaɓe.

Ya ƙara da cewa manufar su ita ce kare dimokuraɗiyya da kuma hana yiwuwar kafa mulkin jam’iyya ɗaya a ƙasar.

Shi ma Peter Obi ya bayyana cewa lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su haɗu domin kare haɗin kai, zaman lafiya da tsaron ƙasa ta hanyar kare tsarin dimokuraɗiyya.

Ana sa ran masu zanga-zangar za su kai ƙorafinsu kai tsaye ga INEC yayin da ake ci gaba da tattakin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata