Shugaban Kwamitin Gyaran Manufofin Kuɗi da Haraji na Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya gargaɗi cewa jinkirta aiwatar da sabbin dokokin haraji bayan 1 ga Janairu, 2026 na iya jefa ma’aikata da ’yan kasuwa cikin matsala a faɗin Nijeriya, musamman a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan bambancin dokokin da Majalisa ta amince da su da waɗanda aka wallafa.
Oyedele ya ce idan ba a aiwatar da dokokin ba, kashi 98 cikin 100 na ma’aikata za su cigaba da fuskantar haraji fiye da kima, yayin da ’yan kasuwa kuma za su rasa rangwamen da dokokin ya tanada, su cigaba da biyan haraji masu yawa, lamarin da ke ƙara musu nauyi tare da tsadar rayuwa ta hanyar boyayyen VAT kan abinci, lafiya da ilimi.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels, Oyedele ya ce maimakon dakatar da dokokin gaba ɗaya, ya fi dacewa a gano sassan da ake zargin an sauya su, a aiwatar da abin da Majalisa ta amince da shi, sannan a gyara kura-kuran da ke ciki ta hanyar gyaran doka, yana mai amincewa cewa akwai wasu sassa da ke buƙatar gyara ta hannun Shugaban Ƙasa.
