An binne tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina.
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, sun halarci jana’izar tare da dubban masu juyayi da suka taru domin karrama marigayin.
Sauran manyan baki da suka halarta sun haɗa da Shugaban Ƙasar Chadi, Muhammed Déby; Shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló; da Firayim Ministan Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine.
Akwai kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; gwamnoni da tsoffin gwamnoni, ministoci da manyan jami’an gwamnatin faɗin ƙasar.
An gudanar da sallar jana’iza a filin jirgin sama na Daura ƙarƙashin jagorancin Babban Limamin Daura, Sheikh Salisu Rabiu.
Tun da farko gawar marigayin ta iso Katsina misalin ƙarfe 2:00 na rana, sannan aka ɗauke shi zuwa Daura ta hanya da misalin ƙarfe 3:40 na rana.
An yi harbin ban girma daga ƙarfe 5:32 zuwa 5:35 na yamma, kuma aka binne marigayin da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.
Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a wani asibiti da ke London.
Gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ta isa Daura
Gawar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ta isa gidansa da ke Daura, garinsa na haihuwa a Jihar Katsina.
An taho da gawar ne daga Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina, inda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓe ta da kansa.
Daily Trust ta ruwaito za a fara shigar da gawar cikin gidan don iyalansa da danginsa na kusa su yi masa bankwana na ƙarshe.
Bayan ɗan lokaci a gidan, an ɗauki gawar zuwa filin salla domin gudanar da sallar jana’iza.
Gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ta isa Katsina
Gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ta isa jihar Katsina domin yi mata jana’iza a mahaifarsa da ke Daura.
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne tare da tawagarsa suka rako marigayin daga birnin Landan zuwa Nijeriya.
Kowane lokaci Shugaba Bola Tinubu zai sauka a filin jirgin saman Katsina, yayin da ake dakon isowar gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari

Labari cikin hotuna:
Wasu daga cikin fuskokin manyan shugabannin Nijeriya a filin jirgin saman Katsina, da suka hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin da kakakin majalisar wakilai Tajudden Abbas da, gwamnonin jihohin Zamfara da Jigawa da wasu da dama
Tawagar Jamhuriyar Nijar ta isa Katsina domin halartar jana’izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari

Hotuna: DCL Hausa
An fara haƙar kabarin margayi Muhammad Buhari a gidansa dake Daura

- Hoto: Daily Trust/Jami’an tsaro a kofar gidan Buhari
An ƙara tsaurara matakan tsaro a gidan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, da ke Daura, garinsa a Jihar Katsina, a daidai lokacin da ake sa ran isowar jirgin da ke ɗauke da gawarsa daga birnin London.Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda zai karɓi gawar da kansa a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, tun da farko ya aika Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, zuwa Birtaniya domin rakiyar dawowar gawar zuwa gida.Da wakilin jaridar Daily Trust ya kai ziyara gidan Buhari da ke Daura a safiyar Talata, ya tarar da jami’an hukumar DSS da sojojin Nijeriya na tsaye a bakin ƙofar shiga gidan.Wani majiya da ya fito daga cikin gidan ya tabbatar wa Daily Trust cewa an riga an fara haƙa kabarin marigayin.
Gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ta bar Landan zuwa Daura da safiyar yau

- Jirgin Saman Nijeriya
Gawar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ta bar birnin London da safiyar Talata zuwa Daura, Jihar Katsina, domin gudanar da jana’izarsa.Jaridar PUNCH Online ya bayyana cewa an ɗauko gawar tsohon shugaban ƙasar ne a cikin jirgin sojin saman shugaban Nijeriya, tare da wata babbar tawagar gwamnatin tarayya da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ke jagoranta.A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tarbi gawar tsohon shugaban ƙasa a Katsina kafin a kai shi Daura domin yi masa sutura.Ministan yaɗa labarai da wayar da kan kama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja.A cewar Idris, ana sa ran gawar Buhari za ta isa Najeriya da misalin ƙarfe 12 na rana ranar Talata.







