Kakakin majalisar wakilai Rt. Abbas Tajudeen, ya ce ya janye kudurin dokar tilasta wa kada kuri’a a lokacin zaben kasar, wanda ya dauki nauyin gabatarwa tare da dan majalisa Daniel Adama Ago.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Abdullahi Krishi ya fitar a ranar Litinin, shugaban majalisar ya bayyana cewa, ya yanke shawarar janye kudirin yin gyara ga dokar zabe ta 2022.
A cewarsa, sun gabatar da kudirin ne da kyakkyawar niyya, domin karfafa huldar jama’a da kuma karfafa dimokuradiyyarmu ta hanyar karfafa masu kada kuri’a don su fito su yi zabe.
