Ministan Raya Matasa, Ayodele Olawande, ya shawarci matasan da ke shirin fita aikin NYSC da su mayar da hankali wajen koyon sabbin sana’o’i domin dogaro da kai.
A taron kammala horo na Next Gen RESCO da hukumar samar da lantarki a karkara REA ta shirya, ya ce wajibi ne a sauya tunanin cewa aikin shekara daya kawai na yi wa kasa hidima, domin akwai damar koya da fadada kwarewa.
Shugaban REA, Abba Aliyu, ya bayyana cewa shirin ya horas da matasa 120 kan harkar makamashi mai tsafta tare da burin samar da karin 1,200 a shekaru goma masu zuwa.
