DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 23, 2026
HomeLabaraiDSS da 'yan sandan Nijeriya sun damke wasu mutane 20 da ake...

DSS da ‘yan sandan Nijeriya sun damke wasu mutane 20 da ake zargi da yin kutse a sakamakon jarabawar JAMB

By Salim Muhammad Gali

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS hadin gwiwa da ‘yan sandan Najeriya sun cafke wasu mutane 20 a Abuja, bisa zargin su da kutse a sakamakon jarabawar JAMB ta shekarar 2025.

Hukumar DSS da ’yan sanda sun bayyana cewa mutanen da aka kama na daga cikin wasu gungun masu laifi da ake zargin sun fi mutum 100, wadanda suka kware wajen kutsawa cikin kwamfutocin cibiyoyin shirya jarabawa kamar JAMB da NECO domin sauya sakamako ko yin damfara.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa wadanda aka kama sun aikata wannan laifi ta hanyar kutse a cibiyar na’urorin JAMB lokacin da ake zana jarabawar bana.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata