Thursday, April 9, 2026
HomeBabban LabarinmuKashim Shettima na jagorantar taron majalisar tattalin arzikin kasa

Kashim Shettima na jagorantar taron majalisar tattalin arzikin kasa

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima na jagorantar taron majalisar tattalin arzikin kasar a Abuja.

Wannan shi ne karon farko da ake gudanar da taron, tun bayan zaman da shugaba Tinubu ya jagoranta kan batun kirkirar ‘yan sandan jihohi, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Taron dai wanda aka fara shi da misalin karfe 11:30 na safiyar Alhamis, ya kunshi gwamnonin Najeriya, gwamnan babban bankin kasar da kuma wasu ministoci domin samarwa da tattalin arzikin kasar ingantacciyar makoma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata