Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKimar Nijeriya ta dawo a idon duniya cikin mulkin Shugaba Tinubu na...

Kimar Nijeriya ta dawo a idon duniya cikin mulkin Shugaba Tinubu na tsawon shekaru biyu, in ji fadar shugaban kasa

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce manufofin tattalin arziƙin gwamnatinsa sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda tattalin arziƙin ƙasar ya fara daidaita tare da jawo mata kima a idon duniya.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi bakuncin Sarkin Ogbomosoland, Oba Ghandi Afolabi Oladunni Olaoye, tare da wasu sarakunan gargajiya a fadarsa da ke Abuja.

Ya ce cin hanci da rashawa sun lalata tattalin arziƙin ƙasar, amma yanzu saboda matakan da aka dauka kasar ta fara farfadowa.

Shugaban ya kuma bayyana kafa asusun NELFUND a matsayin matakin tabbatar da cewa babu wani ɗalibi zai daina karatu saboda talauci, yana mai cewa ilimi shi ne makami mafi dacewa wajen yakar talauci.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

  1. Gaskiya wannan Maganar ta Mr. T-Pain Ƙarya Tsagwaronta, saboda Talakawan Nigeria sun shiga Hali na Ƙuncin da basu taɓa shiga ba. Sakamakon Manufofin marasa amfani ga Talaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata