Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedKo da Atiku da Obi sun yi maja ba za su iya...

Ko da Atiku da Obi sun yi maja ba za su iya kayar da Tinubu ba – Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ce ba wata haɗaka da ‘yan adawa Atiku Abubakar tsohon shugaban kasa da Peter Obi tsohon gwamnan Anambra za su yi, da za ta iya zama barazana ga sake zaben Shugaba Tinubu a shekara ta 2027.
Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC na kasa Bala Ibrahim ne ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar Punch.
Bala Ibrahim na mayar da martani kan kalaman mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe cewa, mai gidansa Atiku da Obi sun dauki darasin abinda ya faru a zaɓen da ya gabata kuma za su hada kai domin kawar da gwamnatin APC.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata