Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuKotu a Abuja ta nemi a kawo karshen tuhumar da ake yi...

Kotu a Abuja ta nemi a kawo karshen tuhumar da ake yi wa kanal Dasuki cikin kwanaki 45

Wata Babbar kotun tarayya a Abuja ta sanya ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba don gwamnatin tarayya ta kammala shari’ar tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki game da tuhumar mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma almundahanar kudi.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce mai shari’a Peter Lifu ne ya bayar da wannan umarnin, bayan ya amince da bukatar gwamnati ta dage zaman don kawo karin shaidu, tare da bai wa wanda ake tuhuma damar kare kansa.

Shaida daga hukumar tsaron na farin kaya DSS Monsur Mohammed, ya tabbatar da cewa sun gudanar da bincike a gidajen Dasuki a biranen Abuja, Kaduna da Sokoto, inda suka samu makamai da wasu kayayyaki ciki har da kwamfuta, wayoyi, da takardun banki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata