Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuKotu a Kano ta yi hukunci kan wasu mutane da suka bar...

Kotu a Kano ta yi hukunci kan wasu mutane da suka bar awakinsu suka lalata shuke-shuken gwamnati

Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta gurfanar da Usman Abdullahi da wasu mutune hudu a gaban kotu, bisa zarginsu da laifin barin awakinsu na yawo barkatai har suka lalata shuke-shuken da gwamnati ta dasa a gefen titunan Lodge Road da Race Course Road.

Lauya Mai gabatar da kara Barista Bahijjah H. Aliyu ce ta shigar da ƙarar, inda ta tabbatar wa kotu cewa waɗanda ake tuhumar sun karya sashe na 7(e) na Dokar Lafiyar Jama’a ta Jihar Kano ta shekarar 2019, wadda ta haramta duk wani aiki da zai haifar da cikas ga muhalli ko lalata kayan more rayuwar jama’a.

A wata sanarwar da ma’aikatar muhalli ta Jihar Kano ta fitar ta ce, an dai kama Awaki guda goma sha bakwai mallakar waɗanda ake tuhuma an bar su suna yawo ba kulawa, lamarin da ya janyo suka lalata tsirrai masu ƙawata gari da tace iska da gwamnatin jihar ta shuka don ƙara ingancin rayuwa a birnin.

Kotu ta same su da laifin da ake tuhumarsu da shi tare da yanke musu hukuncin ɗaurin wata ɗaya a gidan yari, ko kuma su biya tarar naira dubu 25 kowannensu. Haka kuma an umarce su da su haɗa kai su biya naira dubu 100 a matsayin diyya ga barnar da awakinsu suka haifar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata