Wata kotun majistare da ke Nomansland a karamar hukumar Fagge, jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarki Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu bisa zargin satar wayar matar sarkin, da kudade da wasu kayayyaki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wadanda ake tuhuma sun hada da Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini, inda aka gurfanar da su kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hadin baki, sata da karbar kayan sata.
Mai gabatar da kara, Barista Abubakar Ibrahim, ya bayyana wa kotu cewa Sulaiman, wanda ke aiki a matsayin direban matar Sarki Sanusi, ya shiga dakinta ba bisa ka’ida ba, ya sace kayayyakin da aka kiyasta kudinsu ya kai naira miliyan 60, tare da wasu kudade da wayar salula.
A lokacin da aka karanta tuhume-tuhumen, Sulaiman ya amsa laifi, yayin da sauran biyun suka musanta. Koda yake Lauyan wadanda ake tuhuma, Barista A.A. Abdullahi, ya gabatar da bukatar beli.
Alkalin kotun, Mai shari’a Halilu Abdurahman, ya amince da bayar da beli ga wadanda ake tuhuma tare kuma da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu, sai dai za a ci gaba da tsare su har sai sun cika sharuddan belin.
