Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuKotu ta ba da Emefiele beli kan Naira biliyan 2

Kotu ta ba da Emefiele beli kan Naira biliyan 2

Babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Mai shari’a Halilu Yusuf, ta bayar da belin Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, a kan kudi naira biliyan 2.

Emefiele ya bayyana a gaban kotu ne ranar Litinin, 16 ga Yuni, inda ake tuhumarsa da laifuka takwas da suka hada da mallakar kadarori har 753 da kuma zambar biliyoyin Naira.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa kotun ta shar’anta dalilan samun belin ya kasance idan ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa, kuma dole su kasance da kadarorin da darajarsu ta kai akalla biliyan 2 a unguwannin Asokoro, Maitama ko Wuse 2 a cikin Abuja.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata