Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedKotu ta matsar da yanke hukunci kan karar neman raba Ganduje da...

Kotu ta matsar da yanke hukunci kan karar neman raba Ganduje da kujerar shugabancin APC na kasa

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage zaman yanke hukunci kan karar da wasu ‘yan Arewa ta tsakiyar Nijeriya suka shigar, suke neman a karbe shugabancin jami’iyyar APC na kasa daga hannun Abdullahi Umar Ganduje a maido musu mukamin a yankinsu.
DCL Hausa ta rawaito cewa a ranar 5 ga watan Yuli, Mai shari’a Inyang Ekwo ya saka ranar 18 ga watan Satumbar, 2024 don yanke wannan hukunci. Amma kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya ba da labarin cewa kotun ta mayar da 23 ga Satumba a matsayin sabuwar ranar yanke hukuncin.
NAN ya gano cewa bangarorin da shari’ar ta shafa sun samu sako daga kotun cewa an zakuda ranar zuwa 23 ga wata, saboda ba a kammala harhada bayanan hukuncin ba.
Kungiyar magoya bayan jami’iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya karkashin jagorancin Hon Saleh Abdullahi Zazzaga ne dai ke kalubalantar Abdullahi Ganduje a matsayin Shugaban APC na kasa, alhali ba daga yankin Arewa ta tsakiya ya fito ba, mukamin da suke cewa nasu ne bayan saukar Abdullahi Adamu.
A cikin karar, ‘yan yankin na arewa ta tsakiyar Nijeriya na kalubalantar Abdullahi Ganduje, jami’iyyar APC da hukumar zaben INEC kan shugabancin jami’iyyar na kasa.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata