DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedKotu ta umarci gwamnatin Rivers da ta biya al'ummar da aka yi...

Kotu ta umarci gwamnatin Rivers da ta biya al’ummar da aka yi wa rusau ba bisa ka’ida ba diyyar sama da Naira biliyan 1

Jihar Rivers 

Wata babbar kotu a jihar Rivers ta bawa gwamnatin jihar umarnin cewa ta biya diyyar Naira biliyan 1 da miliyan 100 ga mutanen da aka rushewa kadarorinsu ba bisa ka’ida ba a Mile One da Mile Two da ke karamar hukumar Fatakwal.

Da yake yanke hukunci a Larabar nan mai shari’a Sika Aprioku, yace gwamnatin ba ta sanar da al’ummar da abin ya shafa ba kafin ta yi rusau din, inda ya ce, kotun ta samu gwamnati da laifin kwace musu filayensu da karfi.

Tun a shekarar 2022 ne dai, mazauna jihar da abin ya shafa, suka shigar gwamnatin kara gaban kotu bisa zargin tauye hakkokinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata