Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKotu ta umurci bankuna 6 su bayar da bayanai kan asusan Omoyele...

Kotu ta umurci bankuna 6 su bayar da bayanai kan asusan Omoyele Sowore

Wata Babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya, ta umurci bankuna guda shida su mika wa Sufeto Janar na ‘yan sanda bayanan asusun Omoyele Sowore tun daga watan Janairu 2024 zuwa yanzu.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni bayan mika bukatar neman izinin yin hakan da lauyan IGP Wisdom Madaki ya yi.

Jaridar Daily Nigerian ta ce ’yan sanda na zargin Sowore, wanda shi ne mai kafar Sahara Reporters da hannu a harkokin ɗaukar nauyin ta’addanci, wanke kuɗi da kuma wasu ayyukan zamba.

Bankunan da abin ya shafa sun haɗa da: UBA, GTBank, Zenith Bank, Opay, Moniepoint da Kuda Microfinance Bank.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya nuna cewa sama da asusun banki 26 da ake dangantawa da Sowore ne kotu ta bayar da umarni a bincika domin taimaka wa jami’an tsaro wajen gudanar da nasu bincike.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata