Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuKotu ta umurci da a mayar da Natasha Akpoti bakin aikinta na...

Kotu ta umurci da a mayar da Natasha Akpoti bakin aikinta na Sanata a majalisa

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar Dattawa ta janye dakatarwar da ta yi wa sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya.

A watan Maris da ya gabata ne, majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida bisa zargin rashin da’a, bayan sabani da shugaban majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kan sauya zamanta a zauren majalisa.

Sanatar ta zargi Akpabio da yi mata tayin lalata, sannan ta shigar da korafi a gaban Majalisar Dinkin Duniya.

Saidai a rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito mai shari’a Binta ta ce dokar ba ta fayyace adadin kwanakin da za a iya dakatar da dan majalisa ba, kuma la’akari da cewa Majalisa tana da kwanaki 181 na zama a kowace shekara, dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida kamar hana wakilcin mazabarta ne gaba daya.

Bisa wannan dalili, kotun ta umarci majalisar Dattawa da ta dawo da ita nan take domin ci gaba da wakilci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata