Babbar kotu da ke zaune a Warri ta jihar Delta ta umurci rundunar ‘yansandan Nijeriya da Sufeta-Janar na ‘yansanda da su dakatar da dokar hana sa gilashi mai duhu a motoci.
Kotun ta umurci ‘yansandan da su girmama hukuncin kotun har sai yadda hali ya ba da game da shari’ar.
Hukuncin wanda kotu ta yi na wucin gadi ya biyo bayan karar da wani lauya mai suna Aikpokpo-Martins ya shigar a kan Sufeta-Janar na ‘yansanda da rundunar ‘yansandan Nijeriya a kan lamarin.
