Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuKotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin zaman gidan yari ko biyan...

Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin zaman gidan yari ko biyan tara kan cin zarafin Naira

Babbar kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin Mai shari’a Simon Amobeda ta yanke wa Murja Ibrahim Kunya hukuncin watanni shida a gidan gyaran hali ko biyan tarar Naira 50,000, bayan ta amsa laifin cin zarafin Naira.

EFCC ce ta gurfanar da Murja a watan Janairun 2025 bisa karya dokar CBN da ta haramta cin zarafin Naira. An bayar da belinta, amma ta ki bayyana a kotu har sai da aka sake kama ta a ranar 16 ga Maris 2025.

An sake gurfanar da ita a ranar 20 ga Mayu, inda ta amsa laifinta, a hukuncin, kotu ta umurce ta zama jakadiyar EFCC da CBN don wayar da kai kan illar cin zarafin Naira ta hanyar shafinta na sada zumunta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata