Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, ta bayar da umarnin dakatar da ci gaba da shari’ar da ake yi a babbar kotun tarayya, wadda Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar, tana kalubalantar dakatar da ita daga majalisar dattawa.
Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin ne ya biyo bayan bukatar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya gabatar, na neman a kara masa wa’adin daukaka kara, kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, a cewar jaridar Premium Times.
A hukuncin da ya yanke a ranar 10 ga Maris, Alkali Obiora Egwuatu, ya umurci shugaban majalisar dattawa da sauran mutane uku da Natasha ke kara, cikin sa’o’i 72 su bayyana dalilin da zai hana kotun dakatar da duk wani bincike da ake yi wa Natasha a wancan lokacin.
Sai dai Akpabio ya daukaka kara ta hannun lauyansa, inda yanzu kotun daukaka kara ta dakatar da umurnin na farko.

Allah yaqara ma .Mai wakiltar kogi lafiya shikuma korto Allah ya hadashi da masifa