A wannan Talatar ne Kotun Koli a Nijeriya za ta saurari karar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kasar, David Mark, ya shigar, kan karar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafiu Bala, ya shigar dangane da rikicin shugabancin a jam’iyyar.
A cikin karar, David Mark na rokon kotu da ta dakatar da aiwatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara da aka yanke a ranar 12 ga Maris.
Karar, wadda lauyansa Realwan Okpanachi ya shigar, na neman kotun ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin kotun daukaka kara har sai an saurari karar da suka daukaka.
Haka kuma Mark ya roki kotu da ta hana Hukumar Zaben INEC, yin wani sauyi a tsarin shugabancin jam’iyyar na kasa kamar yadda yake a karkashinsa, har sai an kammala sauraron karar.
Bugu da kari, ya kuma nemi kotu ta dakatar da ci gaba da sauraron wata kara da ke gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na Kotun Tarayya da ke Abuja.
Mark ya daukaka kara ne kan hukuncin da Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke a ranar 4 ga Satumba, 2025, dangane da wata bukatar gaggawa da Nafiu Bala ya gabatar.
Jam’iyyar ADC na fama da rikici mai tsanani na bangarori, inda kowane bangare ke ikirarin shi ne halastaccen shugabancin jam’iyyar.
Wannan rikici ya jawo jerin umarnin kotuna da kuma rudani a bangaren gudanarwa kan wanda ke da iko da tsarin shugabancin jam’iyyar na kasa.
Lamarin ya kara dagulewa bayan rahotanni sun ce INEC ta cire sunan David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar a bayanan ta.
Wannan mataki ya haifar da zanga-zanga daga kwamitin ayyuka na kasa da ke goyon bayan Mark, inda manyan jiga-jigan ADC suka halarta, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola; da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi.
Haka kuma, tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, na daga cikin wadanda suka halarci zanga-zangar tare da sauran shugabannin ‘yan adawa a jam’iyyar.
Sai dai a daya bangaren, bangaren da Nafiu Bala ke jagoranta ma ya shirya wata zanga-zanga, inda suke neman INEC ta amince da su a matsayin sahihan shugabannin jam’iyyar.
