DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedKudirin da zai mayar da Nijeriya tsarin mulki mai amfani da 'Prime...

Kudirin da zai mayar da Nijeriya tsarin mulki mai amfani da ‘Prime Minister’ ya zarce karatu na biyu a zauren majalisa

 

Majalisar wakilai

Kudurin da ke neman mayar da Nijeriya tsarin mulki mai amfani da ‘Prime Minister’ ya zarce karatu na biyu a zauren majalisar wakilai a ranar Alhamis.

Kudurin na daga cikin kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya guda 31 da aka zartar domin yin karatu na biyu a zauren da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu ya jagoranta a ranar Alhamis.

Kudirin dokar wanda shugaban marasa rinjaye na majalisa Kingsley Chinda da mambobin majalisar 59 suka goyi baya, na kokarin sauya tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda akai wa kwaskwarima a shekarar 1999, don samar da ofishin Firaminista a matsayin shugaban gwamnati da ofishin shugaban kasa da kuma samar da tsarin yadda za a gudanar da zabe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata