Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuKungiyar gwamnoni da ta dattawan Arewacin Nijeriya za su kafa majalisar ci-gaban...

Kungiyar gwamnoni da ta dattawan Arewacin Nijeriya za su kafa majalisar ci-gaban yankin

Kungiyar dattawa da ta gwamnonin Arewacin Najeriya sun amince da kafa majalisar ci-gaban yankin, wadda za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikinsa.

Matakin ya biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar ci-gaban tattalin arzikin Arewacin Nijeriya a karshen taron zuba hannun jari na masana’antu a yankin da aka kammala a birnin Abuja ranar Litinin.

A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, shugaban taron, Farfesa Ango Abdullahi ya ce, majalisar za ta yi aiki ne karkashin kulawar kungiyoyin biyu domin tabbatar da tsarawa da kuma aiwatar da yadda ci-gaban yankin zai kasance, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata