Ƙungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya (PETROAN) da kuma Ƙungiyar ’Yan kasuwar man fetur masu zaman kansu (IPMAN) sun nemi Shugaba Bola Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki su shiga tsakani kan takaddama tsakanin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) da kamfanin matatar mai ta Dangote.
Sai dai kuma, Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) duk da ita ma tana kira da a gaggauta warware matsalar, ta zargi kamfanin Dangote da rashin mutunta ma’aikata.
Wannan na zuwa ne bayan NUPENG ta bayyana a ranar Juma’a cewa za ta fara yajin aiki daga Litinin, 8 ga watan Satumba.
Takaddamar ta shafi shirin matatar mai ta Dangote na shigo da manyan motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) domin rarraba mai kai tsaye ga ’yan kasuwa.
An tsara fara shirin ne tun ranar 15 ga watan Agusta, amma ya samu jinkiri sakamakon matsalar jigila daga kasar China. Duk da haka, kamfanin ya ce zai fara da zarar motocin sun iso.
A cikin wata sanarwa da shugaban NUPENG, Williams Akporeha, da sakataren ta, Afolabi Olawale, suka sa hannu a ranar Juma’a, ƙungiyar ta zargi matatar mai ta Dangote da keta hakkokin ma’aikata, abin da ta ce na barazana ga rayuwar mambobin reshen Direbobin Tankuna da Motoci na ƙungiyar.
Ƙungiyar ta kuma koka cewa mai kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya nace cewa sabbin direbobin motocin da za a shigo da su ba za a bari su shiga kowace ƙungiya ba.
Kungiyar masu gidajen man fetur ta Nijeriya na shirin shiga yajin aiki
RELATED ARTICLES
Recent Comments
on Gwamnatin Tinubu za ta fara ba da rancen maras kuɗin ruwa ga manoma da masu ƙananan sana’o’i – GEEP
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Jaridar Daily Trust ta gano dalilai uku da suka sa Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC na kasa
on Peter Obi ya sake jaddada bukatar kafa tsarin wa’adin shekara 5 kacal ga shugaban ƙasa a Najeriya
on Cire tsoffin ‘yan sanda daga daga tsarin Contributory Pension Scheme ya fi karfina – IGP Egbetokun
on Gwamnatin Nijeriya ta ɗage buɗe shafin neman aiki na Immigration, Civil Defence da sauran hukumomi
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An karkatar da Naira Bilyan 71.2 daga cikin Bilyan 100 na bashin dalibai a Nijeriya – Hukumar ICPC
on Gwamna Abba Gida Gida ya zabi tsohon shugaban ma’aikatansa da wasu mutum 5 a matsayin kwamishinoni
on Nijeriya za ta zama jagorar kasuwar halal ta duniya mai jarin Dala bilyan Dubu 7 – Kashim Shettima
