Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuKungiyar SERAP ta maka hukumar RMAFC kotu kan shirin ƙara albashin Tinubu...

Kungiyar SERAP ta maka hukumar RMAFC kotu kan shirin ƙara albashin Tinubu da gwamnoni

Kungiyar kare hakkin jama’a da tabbatar da gaskiya a harkokin gwamnati (SERAP) ta shigar da ƙara a kotu kan Hukumar Rabon Kuɗaɗe da Tsare-Tsaren Kuɗin Gwamnati (RMAFC) bisa shirin ƙara wa manyan jami’an gwamnati albashi, ciki har da shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu, da kuma ’yan majalisa.

A watan da ya gabata, RMAFC ta bayyana cewa ta na da shirin ƙara wa shugabannin ƙasa da gwamnoni da ’yan majalisa albashi, inda ta ce albashin da ake biyansu a yanzu “kaɗan ne.”

Sai dai a wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Lahadi, ya tabbatar da cewa sun maka hukumar a kotu, duk da cewa har yanzu ba a saka ranar sauraren ƙarar ba.

A ƙarar da aka shigar a makon da ya gabata a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, mai lamba FHC/ABJ/CS/1834/2025, SERAP ta nemi kotu ta tantance ko shirin ƙarin albashin shugaban ƙasa, mataimakinsa, gwamnoni da mataimakansu, da kuma ’yan majalisa bai sabawa doka, kundin tsarin mulki da kuma dokokin RMAFC ba.

Kungiyar ta roƙi kotu ta ayyana cewa shirin ƙarin albashin ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da dokar RMAFC, don haka ya kasance ba bisa ka’ida ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata