Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuKuri'a miliyan 15 Tinubu ke nema daga jihohi 11 domin ya zarce...

Kuri’a miliyan 15 Tinubu ke nema daga jihohi 11 domin ya zarce a 2027 – Jaridar Punch

By Salisu Ado Sulaiman

Binciken jaridar Punch ya nuna cewa jam’iyyar APC na  ci gaba da rajistar sabbin magoya baya a jihohi daban daban na Najeriya.

Wannan ya zo ne a yayin da jam’iyyar ke ci gaba da shirye shiryen tunkarar zaben 2027, inda rassan ta daga jihohi 11 suka sha alwashin bai wa Shugaba Tinubu kuri’u miliyan goma sha biyar domin ba shi damar zarcewa kan wa’adi na biyu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar barazanar siyasa daga bangarorin hamayya masu yunkurin kawar da ita daga mulki a shekarar ta 2027.

Sai dai yayin hira da gidan talabijin na Channels, sabon shugaban APC Nentawe Yilwatda ya bayyana shirin daukar tsauraran matakai domin ci gaba da inganta tafiyar jam’iyyar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata