Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKwalejojin ilimi na tarayya za su fara ba da shahadar digirin farko...

Kwalejojin ilimi na tarayya za su fara ba da shahadar digirin farko a Nijeriya – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta fara aiwatar da tsarin karatu a dukkan kwalejojin ilimi na tarayya, wanda zai bai wa kwalejojin damar ba da takardar shedar malanta a Nijeriya da kuma Digiri na farko a fannin ilimi.

Wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo ya fitar, ya ce wannan ya biyo bayan dokar kwalejojin ilimin tarayya ta 2023 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu.

Da yake kaddamar da tsarin a Abuja, Ministan Ilimi Dokta Tunji Alausa ya nuni da cewa wannan gagarumin ci gaba ne da zai sake fasalin ilimin a Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata