DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiBankin raya Afirka ya kaddamar da shirin bayar da tallafin dala miliyan...

Bankin raya Afirka ya kaddamar da shirin bayar da tallafin dala miliyan 650 ga Najeriya na tsawon shekaru 5

Bankin raya Afirka ya kaddamar da shirin bayar da tallafi na tsawon shekaru biyar ga Najeriya, inda zai rika samar da akalla dala miliyan 650 a kowacce shekara daga 2025 zuwa 2030 a wani yunkuri na kawo ci gaba ga tattalin arzikin kasar.

Kamar yadda wata sanarwa da bankin ya wallafa a shafinsa na yanar gizo ta nuna, shirin zai samar da dala biliyan 2.95 a shekaru hudun farko, yayin da za a karasa ragowar da adadin da yayi hasashen ya kai dala biliyan 3.21.

Kazalika sanarwar ta bayyana cewa shirin na da nufin cike gibin ayyukan ci gaba da Najeriya ke da shi, musamman inganta bangarorin da suka shafi ayyukan tituna, samar da wutar lantarki, samar da ruwan sha mai tsafta, da kuma samar da ayyukan yi sama ga mata da matasan kasar.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata