Kungiyar Amnesty International ta bayyana damuwa kan tsare Hamdiyya Sidi Sharif da ‘yan sanda ke yi a Zamfara, duk da cewa ta na bukatar kulawar gaggawa bayan sace ta, yayin da rundunar ‘yan sandan Sokoto ke matsa lamba a mika ta gare su.
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, na na ci gaba da fuskantar suka kan yadda yake murkushe masu sukar gwamnatinsa, wanda ko a zaman kotun na watan Janairu, lauyan Hamdiyya, Abba Hikima, ya nemi kariya daga ‘yan sanda saboda barazana a kotu, kuma kotun ta amince.
Amnesty ta ce maimakon murkushe masu sukar gwamnati, kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke addabar yankin gabashin Sokoto, inda ‘yan bindiga ke neman rayuwar mutane, kona kauyuka da sace mata da yara kusan kullum.

Allah duk Wanda yake da hannun cikin jefa hamdiyya cikin halin da take ciki Allah kayi masa fiye da abunda yayi mata idan Mai Mulki ne ya Allah ka kwace mulkinsa Kuma kajarafce shi dason Mulki Kuma kanashi
Gaskiya wnnnan kasa tamu Nigeria saidai Allah yagyara Mana ita Amma fisabilillahi menene amfanin riqe wannan yarinyar bayan abinda tafada Babu tantama hakanne sannan dokace tabasu dama kokuma kawai zalumcine da aka Saba yiwa talaka?