Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yaba wa magoya bayansa bisa haƙuri, juriya da biyayya da suka nuna duk da ƙalubalen da tafiyar ke fuskanta, yana mai cewa hakan ne ke gina kyakkyawar makomar Kwankwasiyya akidar.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya fitar a ranar Litinin, inda ya nuna jin daɗinsa ga magoya baya da masoya tafiyar bisa ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufofin Kwankwasiyya a lokutan da suke fuskantar ƙalubale.
Kwankwaso ya jaddada cewa ƙarfin Kwankwasiyya na ta’allaka ne kan tsantsar biyayyar mabiyanta, gaskiya da ci gaban al’umma, ko da a lokacin matsin lamba.
