DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedMa'aunin tattalin arziki GDP na Nijeriya ya karu da kashi 3.46 -...

Ma’aunin tattalin arziki GDP na Nijeriya ya karu da kashi 3.46 – hukumar kididdiga NBS

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce ma’aunin tattalin arzikin Nijeriya ya karu zuwa kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, inda ya kai naira tiriliyan 71.1.
Wani bayani da Shugaban hukumar kididdiga ta kasa Prince Adeyemi Adeniran Adedeji, ya ce an samu ci gaba da kashi 0.92 idan aka kwatanta da rubu’i na uku na shekara ta 2023 da ma’aunin GDP ya kai kashi 2.54.
Bayanin ya kara da cewa ma’aunin a rubu’i na uku ya yi sama da kashi 0.27 idan aka kwatanta da rubu’i na biyu na wannan shekara ta 2024.
Wannan ci gaban da aka samu, hukumar kididdiga NBS ta alakanta shi da ci gaban da aka samu fannin noma da kasuwanci da sadarwa da kuma harkar gidaje.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata