Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuMajalisa ta yi watsi da bukatar tsarin karba-karba a shugabancin Nijeriya

Majalisa ta yi watsi da bukatar tsarin karba-karba a shugabancin Nijeriya

Majalisar wakilan Nijeriya ta ki amincewa da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman a yi tsarin karba-karba a kujerar shugaban kasa da ta mataimakinsa tsakanin yankuna shida na kasar.

Haka kuma, majalisar ta ki amincewa da wasu kudirori shida na gyaran kundin tsarin mulki da aka saka a cikin jerin ajandar zaman majalisar a ranar Talata.

Sai dai, majalisar ta yanke shawarar dawo da wadannan kudirori a ranar Laraba domin ci gaba da nazarinsu daya bayan daya bisa cancantarsu ta musamman.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata