Majalisar dokokin Nijeriya ta kayyade Naira biliyan 10 ga masu takarar shugaban kasa da Naira biliyan 3 ga masu takarar Gwamna a matsayin adadin kudin da za a kashe wajen yakin neman zabe a kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na daga cikin kudurin gyaran dokar zabe ta shekarar 2025, bayan yin la’akari da rahoton kwamitin da ke kula da harkokin zabe na majalisar ya gabatar karkashin jagorancin Adebayo Balogun.
Kazalika an amincewa masu neman kujerar Sanatoci su kashe Naira miliyan 500 sabanin miliyan 100 a baya, sai kuma ‘yan majalisar wakilai Naira miliyan 250 daga miliyan 70.
Ga majalisun jihohi kuwa, Naira miliyan 100 aka amince daga miliyan 30, sai masu neman shugabannin kananan hukumomi Naira miliyan 60 daga miliyan 30, baya ga kansiloli da ya kasance Naira miliyan 10 daga miliyan 5.
