Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuMajalisar wakilai na shirin yin kudirin sanya kotun daukaka kara ta zama...

Majalisar wakilai na shirin yin kudirin sanya kotun daukaka kara ta zama matakin karshe a shari’o’in zaben gwamna Wani dan Majalisar Wakilai, Bayo Balogun, ya ce majalisar tana aiki kan kudirin gyara kundin tsarin mulki na 1999 domin sanya Kotun Daukaka Kara ta zama matakin karshe a shari’o’in zaben gwamna, ba tare da kai kara zuwa Kotun Koli ba. Balogun, wanda shi ne shugaban kwamitin INEC a majalisar, ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV, inda ya ce kudirin zai rage lokacin sauraron karar zabe daga kwana 90 a kotun farko zuwa kwana 50 a matakin daukaka kara, tare da takaita lokacin gabatar da kara da daukaka kara. Ya kara da cewa, idan aka amince da kudirin, INEC za ta gudanar da zabukan gwamna da wuri don kammala shari’o’in zabe kafin karewar wa’adin gwamnoni, kuma za a rage matakan sauraron kara daga uku zuwa biyu kacal.

Majalisar wakilai na shirin yin kudirin sanya kotun daukaka kara ta zama matakin karshe a shari’o’in zaben gwamna

Wani dan Majalisar Wakilai, Bayo Balogun, ya ce majalisar tana aiki kan kudirin gyara kundin tsarin mulki na 1999 domin sanya Kotun Daukaka Kara ta zama matakin karshe a shari’o’in zaben gwamna, ba tare da kai kara zuwa Kotun Koli ba.

Balogun, wanda shi ne shugaban kwamitin INEC a majalisar, ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV, inda ya ce kudirin zai rage lokacin sauraron karar zabe daga kwana 90 a kotun farko zuwa kwana 50 a matakin daukaka kara, tare da takaita lokacin gabatar da kara da daukaka kara.

Ya kara da cewa, idan aka amince da kudirin, INEC za ta gudanar da zabukan gwamna da wuri don kammala shari’o’in zabe kafin karewar wa’adin gwamnoni, kuma za a rage matakan sauraron kara daga uku zuwa biyu kacal.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata