Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedMajalisar wakilan Nijeriya ta yi kira ga ministan sadarwa, Bosun Tijani da...

Majalisar wakilan Nijeriya ta yi kira ga ministan sadarwa, Bosun Tijani da hukumar sadarwa ta NCC, da su dakatar da karin kudin sadarwa a kasar

 

‘Yan majalisar wakilai

Wannan ya biyo bayan amincewa da kudurin dan majalisar wakilai Obuku Offorji ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.  

Da yake gabatar da kudirin, ya tunatar da cewa, bayan taron masu ruwa da tsaki a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, ministan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba kamfanonin sadarwa a Nijeriya za su kara farashin kudin sadarwa. 

A cewar ministar, ana ci gaba da tuntubar juna tare da wasu kamfanonin sadarwa a kasar kan karin kudin.

Sai dai ya ce ba za a yi karin kashi 100 ba, kuma hukumar NCC za ta amince da sabon tsarin da za a sanar a gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata