Kungiyar malaman makaranta ta Nijeriya NUT ta yi gargaɗin yiwuwar tsunduma yajin aiki a fadin ƙasar, bayan hare-haren makarantun Kebbi da Niger da suka yi sanadin halaka mutum biyu da sace ɗalibai da dama.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna takaicinta na halaka mataimakin shugaban makaranta da jami’in tsaron da ke kula da makarantar, da kuma sace dalibai 25 a jihar Kebbi.
Haka kuma ta yi Allah wadai da sace sama da dalibai 300 da ma’aikata 12 a jihar Niger, tana mai kiran wadannan hare-haren da ta’addanci kuma abin ƙyama.
NUT ta ce dole gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin dakile sake faruwar irin wadannan hare-haren, domin a cewarta, hakan na iya jefa tsarin ilimi cikin halaka.
