Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuMasu kiran a sauya hafsoshin tsaron Nijeriya na da wata boyayyar manufa...

Masu kiran a sauya hafsoshin tsaron Nijeriya na da wata boyayyar manufa – Ali Ndume

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu, ya roki Shugaba Bola Tinubu da cewa kar ya saurari kiran a sauke manyan hafsoshin tsaron Nijeriya.

A cewarsa, irin wannan kira zai iya karya gwiwar rundunonin soji a daidai lokacin da ake bukatar hakan wajen yaki da ayyukan ta’addanci.

Kungiyar “Northern Ethnic Nationalities Forum” ce ta yi kira a farkon makon nan da a gaggauta sauke hafsoshin tsaro, tana mai cewa ba su da kwarewar da ake bukata wajen shawo kan matsalar tsaro duk da makudan kudaden da ake ware wa bangaren cikin kasafin kudi.

A bangare guda, Ndume ya ce matsalolin tsaron Nijeriya sun fi danganta ne da rashin isassun kayan aiki da kuma rashin kulawa ga walwala sojoji.

Ya jaddada cewa abin da ake bukata shi ne horo, kayan aiki, da kuma kwarin gwiwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata