Friday, April 10, 2026
HomeUncategorizedMataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima zai wakilci shugaba Tinubu a kasar Senegal...

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima zai wakilci shugaba Tinubu a kasar Senegal wajen bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kan kasar

Kashim Shettima

 Mataimakin shugaban kasar Shettima ya bar Abuja ne zuwa Dakar domin ya wakilci shugaba Tinubu a wajen bikin cikar Senegal shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Kasar Senegal na bikin ranar samun ‘yancin kai a ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara, inda ake bikin ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekara ta 1960.

Ranar dai ta kasance cikin alfahari da al’ummar kasar, tare da shagulgula, da yin fareti da wasanni na al’adun kasar.

Halartar mataimakin shugaban kasa a taron na shekara-shekara, don girmama goron gayyatar da shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya biyo bayan kyakkyawar alakar da ke tsakanin Nijeriya da Senegal.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata