Matatar man Dangote ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa ta dakatar da aiki, tana mai cewa aiki na ci gaba da gudana yadda ya kamata ba tare da tsaiko ba.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar 5 ga Janairu, 2026, ya bayyana cewa matatar na samar da lita miliyan 40 zuwa 50 na man fetur (PMS) a kullum, gwargwadon bukatar kasuwa.
Sanarwar ta kara da cewa, a ranar 4 ga Janairu, matatar ta samar da lita miliyan 50 na PMS, inda aka fitar da lita miliyan 48, tare da adadin ajiyar da ke iya wadatar Nijeriya na sama da kwanaki 20.
Kamfanin ya ce ayyukan gyaran na yau da kullum da ake yi a wasu sassa ba sa shafar yawan man da ake samarwa, kuma ana ci gaba da tace man PMS, Dizal da Jet A-1 a dukkan sassan da ke aiki.
Dangote Petroleum Refinery ta ce farashin man fetur daga matatar (ex-gantry) na nan daram a ₦699 kan kowace lita, kuma ana sayarwa ga ‘yan kasuwa da masu sayen kaya masu yawa ba tare da nuna wariya ba.
Kamfanin ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labaran karya, su kuma dogara da ingantattun bayanai, yana mai jaddada kudurinsa na tabbatar da wadataccen man fetur, daidaiton farashi.
