Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuMatsalolin tsaro sun ragu matuka a Arewa — Nuhu Ribadu

Matsalolin tsaro sun ragu matuka a Arewa — Nuhu Ribadu

Mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce hare-haren Boko Haram, ‘yan bindiga da rikicin kabilanci sun ragu matuka a yankin Arewa cikin shekaru biyu da suka gabata karkashin mulkin Bola Tinubu.

Ribadu ya bayyana cewa a lokacin mulkin baya, mutane 1,192 ne aka kashe a Kaduna, yayin da aka sace fiye da 3,348.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ambato Nuhu Ribadu na cewa, fiye da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a Jihar Benue a cikin wannan lokaci.

Saidai gwamnatin na aiki iyakar karfinta wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma da kabilun Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata