Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedMiji da mata sun rasa ransu cikin dare a Kano

Miji da mata sun rasa ransu cikin dare a Kano

Motar hukumar kashe gobara ta jihar Kano 

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar miji da mata sakamakon tashin gobara cikin dare a gidansu da ke yankin Rangaza a ƙaramar hukumar Ungoggo ta Jihar. 

Babban Daraktan hukumar na jihar, Hassan Muhammad ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Juma’a a Kano. 

A cewar sa, gobarar ta tashi cikin daren Alhamis ne, inda ta kone mutumin mai suna Muhammad Uba dan shekara 67 da matarsa Fatima mai shekara 52.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata