Tsohuwar matar shugaban kasa, Maryam Abacha, ta musanta zargin cewa marigayi mijinta, Janar Sani Abacha, ya wawure dukiyar kasa.
A wata hira da aka watsa a tashar TVC don tunawa da shekaru 27 da rasuwarsa, ta ce kudin da ake kira “Abacha loot” ba sata ba ce, kuma ana bata masa suna ne kawai.
Maryam ta bukaci sahihin shaida daga masu zargi, tana mai cewa kudin da mijinta ya adana domin Najeriya sun bace bayan mutuwarsa.
Ta ce kabilanci da bambancin addini ke haddasa cin zarafinsa, kuma ta musanta cewa Abacha ne ya soke zaben 12 ga Yuni.
