Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedMinista Matawalle ya sake kare Tinubu, ya ce mai gidansa ya yi...

Minista Matawalle ya sake kare Tinubu, ya ce mai gidansa ya yi ayyukan ci-gaba a harkar tsaron arewa

Bello Muhammad Matawalle

 

Minista Matawalle ya yi Allah wadai da kalaman da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya yi a kwanakin baya kan burin shugaban kasa Bola Tinubu a 2027.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ya fitar ranar Litinin dinnan a Abuja.

Matawalle ya jaddada cewa shugaba Tinubu ya yi abin yabawa a harkokin mulki kuma Babachir Lawal da mukarrabansa za su yi mamakin irin dimbin goyon bayan da shugaban kasar zai samu daga Arewa.

Ya ce shugaban ya yi abubuwan ci gaba a fannoni daban-daban kamar tsaro, tattalin arziki, ababen more rayuwa da kuma harkokin mulki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata