Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Julius Debrah, ya sanar da hakan ga manema labarai.
Ya ce Ministan tsaro Edward Omane Boamah da ministan muhalli Ibrahim Murtala Muhammed na daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su a kudancin kasar.
Ya kara da cewa tuni shugaban kasar da gwamnati ta mika ta’aziyya da kuma jajantawa iyalansu da kuma sojojin da suka rasa rayukansu wajen yi wa kasar hidima.
Daga cikin wadanda abin ya rutsa da su akwai Alhaji Muniru Muhammad,Deputy National Security Coordinator kuma tsohon ministan noma, da Samuel Sarpong mataimakin shugaban jam’iyyar NDC ta shugaban kasar Mahama.
